Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Safiya Salihu da Halima Abdullahi, mahaifiya da ƙanwar marigayi kasurgumin ɗan ta’adda Kachallah Ibrahim Battujo, hukuncin daurin shekara 20 kowacce saboda laifukan da suka shafi ta’addanci.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan matan sun amsa laifin taimaka wa Battujo da kuma ɓoye bayanai game da ayyukansa. Sai dai an wanke su daga wasu tuhume-tuhume biyu da suka shafi karɓar kuɗaɗen da ake zargin na ayyukan ta’addanci ne.
Mai Shari’a Hauwa Joseph Yilwa ta umarci su yi hukuncin a lokaci guda, sannan bayan kammala zaman yarin za a tura su shirin gyaran hali. Battujo ya mutu ne bayan jami’an tsaro sun kashe shi a wani samame da suka kai a Jihar Kogi.