Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnati za ta kashe N83.2bn don dakile ambaliyar ruwa a Najeriya

Gwamnati za ta kashe N83.2bn don dakile ambaliyar ruwa a Najeriya

Majalisar NEC ta amince da kashe Naira biliyan 83.2 domin dakile ambaliyar ruwa a Najeriya.

Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta amince da ware Naira biliyan 83.2 domin aiwatar da shirye-shiryen kariya daga ambaliyar ruwa da sauran bala’o’in da ake hasashen za su iya faruwa a Najeriya.

An cimma wannan matsaya ne a taro na 158 na majalisar da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya jagoranta a ranar Alhamis.

Rahotanni sun nuna cewa an amince da kudin ne bayan Karamin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya gabatar da bukatar daukar matakan kariya tun kafin aukuwar ambaliya, musamman a wannan lokaci na damina.

Majalisar ta jaddada cewa ya zama wajibi gwamnati ta fi mayar da hankali kan rigakafi maimakon jiran bala’o’i su afku kafin daukar mataki.

Da yake jawabi, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa dole su fara bayyana a zahiri ta hanyar inganta rayuwar al’ummar kasa.

Ya ce nasarar gwamnati ba ta takaitu ga manufofi da aka tsara a takardu ba, sai dai a tasirin da suke yi ga manoma, matasa, masana’antu da sauran ’yan Najeriya.

Shettima ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi su hada kai da gwamnatin tarayya wajen inganta harkar noma da samar da hanyoyin da za su bai wa kayayyakin Najeriya damar shiga kasuwannin duniya cikin sauki.

A cewarsa, bunkasar tattalin arziki ba za ta tabbata ba matukar kasar na ci gaba da fitar da albarkatun kasa ba tare da kara musu daraja ta hanyar sarrafawa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments