Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAn dage tattaunawar Amurka da Iran bayan sabbin hare-haren Isra’ila a Lebanon

An dage tattaunawar Amurka da Iran bayan sabbin hare-haren Isra’ila a Lebanon

An ɗage zaman tattaunawar da aka shirya tsakanin Amurka da Iran a ƙasar Switzerland kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon.

An ɗage zaman tattaunawar da aka shirya tsakanin Amurka da Iran a ƙasar Switzerland kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Switzerland ta tabbatar da cewa an jinkirta taron da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a a Burgenstock, bayan Iran ta dakatar da aika tawagarta saboda hare-haren.

Rahotanni sun ce hare-haren Isra’ila da aka kai cikin daren Alhamis sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 16 a kudancin Lebanon, yayin da ƙungiyar Hezbollah ta ce an gwabza kazamin faɗa a yankin.

A nasa bangaren, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa sojojin ƙasarsa za su ci gaba da kasancewa a yankin tsaro na kudancin Lebanon, yana mai nuna adawa da wasu sassa na yarjejeniyar tsagaita wutar da Amurka da Iran suka cimma, musamman waɗanda suka shafi Lebanon.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments