Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya caccaki masu sukar yarjejeniyar zaman lafiya da Iran

Trump ya caccaki masu sukar yarjejeniyar zaman lafiya da Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kakkausar suka ga masu sukar sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Amurka da Iran.

Trump ya ce duk wanda ke ganin bai ɗora wa Iran tsauraran sharuɗɗa ba, “ko dai mai hassada ne, mugun mutum ko kuma wawa.”

Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta ƙunshi sharuɗɗa 14, ciki har da tsawaita tsagaita wuta, sake buɗe mashigar Hormuz, ci gaba da tattaunawa cikin kwanaki 60 da kuma shirin sake gina Iran tare da sassauta takunkuman da aka ƙaƙaba mata.

Trump ya kuma ce yarjejeniyar ta haifar da sabon tarihi a kasuwar hannayen jari ta Amurka, yayin da farashin danyen mai ya ci gaba da sauka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments