Monday, October 19, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun kashe jami’an tsaron sa-kai biyu a sabon hari a...

Yan bindiga sun kashe jami’an tsaron sa-kai biyu a sabon hari a Plateau

Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kashe akalla jami’an tsaron sa-kai biyu bayan sun kai hari a ƙauyen Rangarasa da ke yankin Rantya, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

Rahotanni sun ce maharan, waɗanda yawansu ya zarce mutum 100, sun iso ne a kan babura a daren Laraba, inda suka rika harbe-harbe domin kutsa cikin garin.

Wani mazaunin yankin, John Mancha, ya ce jami’an tsaron sa-kai sun yi ƙoƙarin dakile harin, amma makaman da ’yan bindigar ke ɗauke da su sun fi ƙarfin waɗanda suke da su.

Lamarin ya sake jefa al’ummar yankin cikin fargaba yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan jihar Plateau.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments