Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin samar da aƙalla megawatt 10,000 na wutar lantarki idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
A wata hira da aka yi da shi, ɗan jarida Rufai Oseni ya tambaye shi dabarar da zai bi wajen cimma wannan buri.
Da yake mayar da martani, Obi ya ce ba zai bayyana yadda zai aiwatar da shirin ba, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne a duba tarihin wanda ya yi alƙawarin.