Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroBindiga kaɗai ba za ta kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya ba –...

Bindiga kaɗai ba za ta kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya ba – Dikko Radda

Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya bayyana cewa yaƙi da ta’addanci ba zai samu nasara ta hanyar amfani da ƙarfin soja kaɗai ba, yana mai cewa dole ne a haɗa hannu tsakanin gwamnati, shugabannin addini, na al’umma da kuma jama’a domin kawo ƙarshen matsalar.

Gwamnan ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta ke yaɗa bidiyo da hotunan hare-haren ‘yan ta’adda, yana mai cewa irin waɗannan wallafe-wallafe na iya taimakawa wajen yaɗa tsoro da kuma bai wa miyagun suna da farin jini da ba su cancanta ba.

Radda ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakai na haɗin gwiwa da suka haɗa da wayar da kai, tattara bayanan sirri da haɗin kan al’umma domin samun nasarar yaƙi da rashin tsaro.

Ya kuma yi bayani kan wasu ƙalubalen da ake fuskanta a Katsina tare da hanyoyin da yake ganin za su taimaka wajen magance matsalar gaba ɗaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments