Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn cafke wani mutum kan zargin tsare ’yar uwarsa tsawon watanni 17...

An cafke wani mutum kan zargin tsare ’yar uwarsa tsawon watanni 17 a Abuja

Kwamishinan ’Yan Sanda na FCT, Ahmed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce an samu labarin lamarin ne a ranar 12 ga watan Yuni.

Kwamishinan ’Yan Sanda na FCT, Ahmed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce an samu labarin lamarin ne a ranar 12 ga watan Yuni.

CP Sanusi ya ce bayan samun rahoton gaggawa, ya tura jami’an bincike daga Sashen Katampe zuwa wurin da abin ya faru.

Ya bayyana cewa bayan isar jami’an, wanda ake zargi ya yi ƙoƙarin hana su shiga gidan, inda ya nuna adawa da binciken ’yan sanda.

Sai dai kwamishinan ya ce wannan ƙin hadin kai bai hana jami’an cika aikinsu ba, domin sun tilasta shiga gidan, inda suka tarar da wacce aka tsare a sarka, cikin matsanancin rashin lafiya da raunin jiki da mummunan yanayin tsafta.

Ya ƙara da cewa an kama wanda ake zargi nan take, yayin da aka garzaya da wacce aka ceto asibiti, inda take ci gaba da samun kulawar likitoci.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya kuma sace ɗan wacce aka tsare ɗin kimanin shekaru biyu da suka gabata, sannan ya ci gaba da tsare ’yar uwarsa domin hana ta yin tambaya kan inda ɗan nata yake.

A cewar rundunar ’yan sanda, ana ci gaba da ƙoƙarin gano inda yaron yake domin ceto shi.

Kwamishinan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike, tare da jinjinawa mazauna yankin bisa bayar da sahihan bayanai da suka taimaka wajen gudanar da aikin ceto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments