Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta kafa kwamitin binciken zargin karkatar da abincin yara masu...

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin binciken zargin karkatar da abincin yara masu tamowa

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani kwamitin musamman domin gudanar da bincike kan zargin karkatarwa, sata da kuma sayar da kayan abincin jinyar yara masu fama da cut art tamowa (RUTF) ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda aka ware domin kula da yara a faɗin jihar.

Yayin ƙaddamar da kwamitin a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin gano gaskiyar abin da ya faru dangane da zargin karkatar da waɗannan muhimman kayayyakin da aka tanada domin ceton rayukan yara.

Ya ce kwamitin zai gudanar da cikakken bincike kan yadda aka yi zargin karkatar da kayan RUTF, tare da gano musabbabin faruwar lamarin da kuma tantance mutanen ko ƙungiyoyin da ake zargin suna da hannu a ciki.

A cewarsa, binciken zai kuma duba yiwuwar sa hannun wasu ma’aikatan lafiya, ’yan kasuwa masu zaman kansu da kuma wasu daga cikin al’umma wajen aikata laifin.

Dakta Abubakar ya ƙara da cewa kwamitin zai tantance adadi da kimar kayayyakin da suka ɓace, tare da gabatar da shawarwari kan matakan da ya kamata a ɗauka domin hana sake aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi sassauci ga duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kayan da aka tanada domin kula da yara masu fama da tamowa ba.

Gwamnatin Kano ta kuma sake nanata aniyarta ta tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma inganta tsarin gudanar da shirye-shiryen kiwon lafiya, musamman waɗanda suka shafi lafiyar yara da sauran masu buƙatar kulawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments