Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiBirtaniya na shirin hana yara masu ƙasa da shekara 16 amfani da...

Birtaniya na shirin hana yara masu ƙasa da shekara 16 amfani da kafafen sada zumunta

Gwamnatin Birtaniya na duba yiwuwar hana yara masu ƙasa da shekara 16 amfani da kafafen sada zumunta a wani yunkuri na ƙara kare su daga matsalolin da ke tattare da amfani da intanet.

Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya bayyana cewa gwamnatin sa na nazarin matakan da za su rage haɗarin da yara ke fuskanta a shafukan sada zumunta, ciki har da tasirin da wasu abubuwa ke yi wa lafiyar kwakwalwa da tarbiyyarsu.

A cewarsa, wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na tabbatar da tsaron yara a duniyar intanet tare da rage haɗurran da ke tattare da amfani da kafafen sadarwar zamani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments