Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiElon Musk ya kafa tarihi bayan ya zama mai Tiriliyan na farko...

Elon Musk ya kafa tarihi bayan ya zama mai Tiriliyan na farko a duniya

Attajirin Amurka, Elon Musk, ya kafa sabon tarihi a duniya bayan da aka bayyana cewa kimar dukiyarsa ta kai kusan dala tiriliyan ɗaya, bisa sabon ƙididdiga da aka danganta da sayar da hannun jarin kamfaninsa na sararin samaniya, SpaceX.

Rahotanni sun nuna cewa SpaceX ta ƙaddamar da sayar da hannun jari Ajin A kusan miliyan 555.6 kan farashin Dala 135 kowanne, lamarin da ya tara kusan Dala biliyan 75 a daya daga cikin manyan cinikin hannun jari da aka taɓa yi a tarihi.

Bayan wannan ciniki, an kiyasta darajar kamfanin ta kai kusan Dala tiriliyan 1.77, wanda ya ƙara ɗaga martabarsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan kamfanonin fasahar sararin samaniya a duniya.

Rahotanni kuma sun nuna cewa Musk zai ci gaba da rike kaso mai yawa na ikon kamfanin, inda yake da kimanin hannun jari Ajin A miliyan 849.5 da Ajin B biliyan 5.57. Wannan ya ba shi ikon sarrafa kusan kashi 84.4% na yanke shawara a cikin kamfanin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments