Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiADC: Har yanzu dimokuradiyya ba ta sauya rayuwar talakan Najeriya ba

ADC: Har yanzu dimokuradiyya ba ta sauya rayuwar talakan Najeriya ba

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kasa amfani da dimokuradiyya wajen inganta rayuwar talakawan Najeriya .

A cikin wata sanarwa da ta fitar domin bikin Ranar Dimokuradiyya, mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ba auna ci gaban dimokuradiyya da yawan shekarun mulkin farar hula kadai ya kamata a yi ba.

A cewar jam’iyyar, abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda tsarin dimokuradiyya ke tasiri wajen bunkasa rayuwar jama’a, rage wahalhalu da samar da walwala ga ’yan kasa.

ADC ta ce duk da shekaru da aka kwashe ana mulkin dimokuradiyya, har yanzu miliyoyin ’yan Najeriya na fuskantar kalubalen tattalin arziki da matsin rayuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments