Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun sace matafiya sama da 20 a Jihar Sokoto

Yan bindiga sun sace matafiya sama da 20 a Jihar Sokoto

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan kasuwa, manoma da matafiya sun fada hannun ‘yan bindiga a kan hanyar zuwa kasuwar Sabon Birni da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun tare babbar hanyar da ke haɗa Sabon Birni da wasu kauyuka da ke kewaye da ita, inda suka kai hari a kan matafiya.

Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun shigo ne da misalin ƙarfe 10 na safe a ranar Laraba, suna kan babura kusan 20, inda suka fara harbe-harbe, abin da ya jefa jama’a cikin tsoro da firgici yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako.

An ce aƙalla mutane 20 ne aka yi garkuwa da su a wannan hari.

Wani daga cikin ‘yan uwan wadanda abin ya shafa, Abdurrashid, ya bayyana cewa mahaifiyarsa tana cikin wadanda aka sace yayin da take aiki a gona.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments