Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroNLC ta goyi bayan yajin aikin malamai kan matsalar tsaro

NLC ta goyi bayan yajin aikin malamai kan matsalar tsaro

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta nuna cikakken goyon baya ga yajin aikin da Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) ke gudanarwa, tana mai cewa matsalar rashin tsaro da yawaitar sace malamai da dalibai sun kai matakin da ba za a iya ci gaba da yin shiru a kai ba.

A cikin sanarwar da shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa matakin da malamai suka dauka ya samo asali ne daga fargaba da kuma hare-haren da suke fuskanta a wuraren aikinsu.

A cewarsa, sace-sacen dalibai da malamai da ake ci gaba da samu, ciki har da lamarin da ya faru a Jihar Oyo, ya nuna cewa matsalar tsaro na kara tsananta a fadin Najeriya.

NLC ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta daukar matakan kare makarantu, malamai da dalibai domin tabbatar da cewa ana gudanar da harkokin ilimi cikin yanayi mai aminci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments