Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya amince da ɗaukar jami'ai 1,000 domin ceto daliban Oyo

Tinubu ya amince da ɗaukar jami’ai 1,000 domin ceto daliban Oyo

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da daukar masu gadin dazuzzuka 1,000 a jihar Oyo tare da tura rundunar musamman mai kwarewa wajen ayyukan ceto domin kubutar da dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Oriire ta jihar.

Matakin ya biyo bayan sace dalibai da malamai daga makarantu uku da suka hada da Community Grammar School, Baptist Nursery and Primary School, da L.A. Primary School a ranar 15 ga Mayu, 2026.

Wata babbar tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila ta kai ziyara zuwa al’ummomin Esiele da Yawota domin jajanta wa mazauna yankin tare da tabbatar musu da cewa gwamnati na daukar dukkan matakan da suka dace domin ganin an kubutar da wadanda aka sace.

A cewar gwamnatin tarayya, za a dauki masu gadin dazuzzukan ne tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Oyo domin karfafa tsaro da sa ido a yankunan dazuzzuka da masu aikata laifuka ke amfani da su a matsayin maboyarsu.

Haka kuma, shugaban kasar ya umarci wata rundunar tsaro ta musamman da ta kara kaimi wajen gudanar da ayyukan ceto cikin gaggawa.

Tawagar ta kuma bayyana cewa bukatar al’ummar yankin na samar da sansanin soji a yankin za a mika ta ga Shugaba Tinubu domin duba yiwuwar amincewa da ita.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an kubutar da daliban da malamai cikin koshin lafiya tare da daukar karin matakan tsaro domin hana sake afkuwar irin wannan lamari a gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments