Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani da ake zargi da jagorantar kungiyar masu aikata laifuka, Ali Bahago Danakulu, tare da wasu mutum biyu da ake zargin mambobin kungiyarsa ne a karamar hukumar Kaura Namoda ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an sashen yaki da manyan laifuka (VCRU) ne suka gudanar da samamen bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan kungiyar da ake zargin tana addabar al’ummomin Kasuwan Daji da kewaye.
A cewarsa, wadanda aka kama sun hada da Ali Bahago Danakulu, Hassan Dan Kure da Dahiru Lawali. Binciken farko ya nuna cewa suna da alaka da wata kungiyar masu dauke da makamai da ake zargin Ali Bahago ne ke jagoranta.
Rundunar ta ce yayin aikin, an hallaka daya daga cikin wadanda ake zargi, yayin da aka kama mutum uku.
Haka kuma, jami’an tsaro sun kwato makamai da kayan aiki daban-daban da suka hada da bindigar pump-action, bindiga kirar G3 da aka kera a gida, wasu bindigogi na gargajiya, harsasai, sarka ta ankwa, bindiga kirar pistol da aka kera a gida, da babura uku.
’Yan sanda sun bayyana cewa wadanda aka kama suna hannunsu domin ci gaba da bincike, yayin da ake kokarin kamo sauran mambobin kungiyar da suka tsere domin gurfanar da su a gaban kuliya.