Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da haƙuri da fatan alheri ga ƙasar, tana mai bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ake fuskanta ba za ta dawwama ba.
Ta ce gwamnatin tarayya na ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da matakan da suka dace domin magance matsalolin tsaro tare da tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Oluremi Tinubu ta kuma jaddada cewa gwamnati na da ƙudirin dawo da zaman lafiya a sassan ƙasar da ke fama da matsalolin tsaro.