Saturday, October 17, 2026
HomeDaga MarubutaYadda Saudiyya ta lalata jiragen sama marasa matuki uku da suka kutsa...

Yadda Saudiyya ta lalata jiragen sama marasa matuki uku da suka kutsa sararin samaniyarta

Saudiyya ta sanar da cewa jami’an tsaron sararin samaniyarta sun dakile tare da lalata jiragen sama marasa matuki guda uku da suka kutsa cikin sararin samaniyar kasar daga bangaren Iraq.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Saudiyya, Turki al-Maliki, ya bayyana cewa an cafke jiragen ne da safiyar Lahadi bayan sun shiga yankin sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.

Ya jaddada cewa Saudiyya na da cikakken ikon kare kanta tare da mayar da martani ga duk wata barazana da za ta iya shafar tsaro da ikon cin gashin kanta.

A cewarsa, gwamnatin Saudiyya za ta dauki duk matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga duk wani hari ko kutse.

Tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya ya kara tsananta tun bayan hare-haren da Amurka da Israel suka kai wa Iran a watan Fabrairu, lamarin da ya janyo ramuwar gayya daga Tehran kan wasu kasashe da cibiyoyi masu alaka da Amurka da Isra’ila.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta kai hare-hare kan wasu wurare a yankin Tekun Fasha tare da rufe mashigar Strait of Hormuz, abin da ya kara dagula harkokin tsaro da tattalin arziki a yankin.

A wani bangare kuma, wani harin jirgi mara matuki ya haddasa gobara a kusa da tashar makamashin nukiliya ta Barakah da ke Abu Dhabi, sai dai hukumomi sun ce babu asarar rai ko wata barazana ga lafiyar muhalli.

Hukumomin Abu Dhabi sun tabbatar da cewa jami’an agajin gaggawa sun shawo kan gobarar cikin gaggawa domin hana yaduwar ta zuwa sauran sassan cibiyar makamashin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments