Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiPeter Obi na fuskantar barazanar rasa goyon bayan ‘Obidient Movement’.

Peter Obi na fuskantar barazanar rasa goyon bayan ‘Obidient Movement’.

Wata ƙungiyar siyasa da a baya take goyon bayan Peter Obi, wato Obidient Movement, ta bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na iya rasa goyon bayanta a zaɓen 2027.

Wata ƙungiyar siyasa da a baya take goyon bayan Peter Obi, wato Obidient Movement, ta bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na iya rasa goyon bayanta a zaɓen 2027.

Mai kula da ƙungiyar, Ikenna Azomchine, ya bayyana hakan a birnin Awka na jihar Anambra, inda ya ce Obi ya yi watsi da mambobin ƙungiyar bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lokacin da ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party.

Azomchine ya ce ƙungiyar za ta wayar da kan jama’a domin su ƙi goyon bayan duk wani ɗan majalisar tarayya da ya samu nasara da sunan Obi amma yanzu bai cika burin al’umma ba.

Yayin da yake ganawa da manema labarai tare da sauran shugabannin ƙungiyar, ya ce manufarsu ita ce tabbatar da nagartaccen shugabanci, kuma ba za su goyi bayan wani takamaiman ɗan takara ko jam’iyya ba.

Ya bukaci masu zaɓe da su zaɓi ‘yan takara daga kowace jam’iyya muddin suna da ƙwarewa da gaskiya.

Ya kuma ce, “Muna sanar da mambobin Obidient Movement cewa su fita zaɓe mai zuwa su zaɓi mafi cancanta. Muna da ma’aunin tantance nagarta da ƙwarewa, kuma mun taba yin hakan a baya.”

Ya ƙara da cewa mambobin ƙungiyar suna shiga ne da son rai, kuma hakan zai ci gaba.

A cewarsa:
“Peter Obi misali ne na irin shugabannin da muke so, amma ba shi ne ke ɗaukar nauyin ƙungiyarmu ba, kuma ba mu da biyayya ga wata jam’iyya. Abin da muke nema shi ne shugabanci nagari da ‘yan siyasa masu koyi.”

Ya jaddada cewa ƙungiyar na kallon Peter Obi a matsayin alama ta sauyi, amma ba shugabanta kai tsaye ba.

Sannan ya yi gargaɗin cewa, Peter Obi na iya rasa goyon bayanmu idan bai yi abubuwan da suka dace ba, domin ba za mu ci gaba da ɗaukar nauyin ƙungiyar saboda shi ba. Yana kuskuren ɗaukar goyon bayan kafafen sada zumunta a matsayin kuri’un gaskiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments