Amfani da miyagun ƙwayoyi na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke barazana ga lafiyar matasa da makomar al’umma a duniya baki ɗaya. Miyagun ƙwayoyi sun haɗa da giya, taba sigari, cannabis, tramadol, codeine da sauran abubuwan da ke lalata kwakwalwa da jiki tare da haddasa matsalolin tunani da na zamantakewa.
Duk da cewa bincike ya nuna cewa matasan wannan zamani na Generation Z suna rage amfani da taba sigari da giya idan aka kwatanta da tsofaffin ƙarni, har yanzu matsalar amfani da miyagun ƙwayoyi tana ci gaba da addabar matasa musamman a Najeriya.
Masana sun bayyana cewa wayar da kai kan lafiya, yawaitar amfani da intanet, da kuma kamfen ɗin hana shaye-shaye sun taimaka wajen rage amfani da wasu tsoffin nau’o’in miyagun ƙwayoyi.
Sai dai kuma ana samun karuwar amfani da sababbin hanyoyin shaye-shaye kamar vaping da haɗa ƙwayoyi masu illa.
Mai magana da yawun Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Kano,Abubakar Sadiq Maigatari, ya tabbatar da cewa matasa ne suka fi yawa a cikin waɗanda ake kamawa da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
A cewarsa:
“Hakika matasa ne suka fi yawa cikin waɗanda ake kamawa da laifin ta’amuli da miyagun ƙwayoyi a jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Duk lokacin da jami’an NDLEA suka fita aiki, idan aka kama mutum ɗari, kusan kashi tamanin matasa ne.”
Ya ƙara da cewa duk da haka, idan aka kwatanta shekaru goma da suka gabata zuwa yanzu, ana samun raguwar adadin matasan da ke shiga cikin matsalar shaye-shaye a hankali sakamakon wayar da kai da kuma ƙoƙarin hukumomi da iyaye.