Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira Uba a jihar Borno, inda ake fargabar sun sace ɗalibai da dama.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9.00 na safiyar ranar Juma’a a makarantar Mussa Primary da Junior Secondary School da ke al’ummar Mussa, kusa da dajin Sambisa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙungiyar matasan Borno ta Kudu, Samaila Kaigama, ya ce maharan sun shiga makarantar tare da sace yaran.
Ya ce, “Eh, sun zo da safiyar yau, sun tafi da wasu yara amma har yanzu ba a san adadinsu ba. Na samu sahihin bayani cewa waɗanda suka sace yaran su ne suka aikata satar mutane a Ngoshe.”
Kaigama ya ƙara da cewa yaran da aka ɗauka ɗaliban makarantar jeka-ka-dawo ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya ce rundunar ba ta samu cikakken bayani kan lamarin ba tukuna.