Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yaba da shirin Airbus na kafa cibiyar gyaran jiragen sama...

Tinubu ya yaba da shirin Airbus na kafa cibiyar gyaran jiragen sama a Najeriya

Tinubu da Airbus sun tattauna kan tsaro da bunƙasa sufurin jiragen sama a Nijeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna jin daɗinsa kan shirin kamfanin Airbus na kafa cibiyar gyaran da kula da jiragen sama a Najeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin wani babban mataki da zai taimaka wajen haɓaka fannin sufurin jiragen sama da tsaro a ƙasar.

Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na cikin matsananciyar buƙatar ƙarin jiragen yaƙi masu saukar ungulu da jiragen yaƙi masu fikafikai domin ƙarfafa yaƙi da ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.

Shugaban ya yi wannan bayani ne yayin wata ganawa da jami’an kamfanin Airbus a taron Africa CEO Forum da aka gudanar a Kigali, babban birnin Rwanda.

A yayin tattaunawar, Tinubu ya buƙaci kamfanin da ya hanzarta miƙa jiragen Apache guda uku da Najeriya ta saya domin amfani da su wajen ayyukan tsaro a faɗin ƙasa.

Bangarorin biyu sun kuma tattauna yiwuwar faɗaɗa haɗin gwiwa a ɓangaren jiragen yaƙi, sayen jiragen Airbus C-295, da kuma hanyoyin samar da kuɗaɗen saye da hayar jiragen sama ga kamfanonin cikin gida.

Shugaban ya kuma bayyana shirin gwamnati na duba yiwuwar kafa kamfanin bayar da hayar jiragen sama domin tallafa wa harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya.

A nasa ɓangaren, shugaban tawagar Airbus, Thierry Cloutet, ya yabawa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu tare da nuna aniyar kamfanin na ci gaba da haɗa kai da Najeriya a harkokin sararin samaniya da jiragen sama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments