Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDakaru sun fatattaki ‘yan ta’adda, sun ceto mutanen da aka jikkata a...

Dakaru sun fatattaki ‘yan ta’adda, sun ceto mutanen da aka jikkata a Sokoto

Dakarun rundunar sojin Najeriya tare da jami’an hukumar DSS sun fatattaki wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne yayin wani samame na tsaro a ƙaramar hukumar Isa da ke jihar Sokoto.

Majiyoyin tsaro sun ce an gudanar da aikin ne da misalin ƙarfe 2:50 na daren ranar 14 ga watan Mayu bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’adda a kusa da ƙauyen Lugu.

Rahotanni sun ce dakarun sun yi artabu da maharan masu ɗauke da makamai, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa yankin Bafarawa.

Bayan artabun, dakarun sun ci gaba da gudanar da bincike a yankin Danzanke da ke ƙauyen Modachi da kuma gefen wani kogi kusa da gadar da ta lalace a yankin.

A yayin aikin, dakarun sun ceto wani farar hula da ya samu raunin harbin bindiga.

“An garzaya da wanda ya jikkata domin samun kulawa a asibiti, yayin da jami’an tsaro suka ci gaba da sintiri da bincike a yankunan domin bibiyar waɗanda suka tsere da kuma hana sake aukuwar ayyukan ta’addanci,” in ji majiyoyin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments