Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sun miƙa takardun neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a hedikwatar ADC da ke Abuja domin zaɓen shekarar 2027.
Atiku ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka wani muhimmin ci gaba ne na dawo da arziki da kyakkyawan fata ga Najeriya. Ya ce wannan ba kawai neman mulki ba ne, illa wata tafiya ta ceto ƙasa da sake gina ta domin amfanin al’umma baki ɗaya.
Shi ma Amaechi ya ce ya shiga takarar ne domin ceto Najeriya daga halin da take ciki, yana mai jaddada cewa idan aka ba shi dama, zai iya sauya ƙasar cikin shekara huɗu. Ya ce ƙwarewa, gogewa da iya aiki ne ya kamata su zama ma’aunin zaɓen shugaban ƙasa, ba batun yanki ko ƙabila ba.
Miƙa takardun nasu na nuna fara fafatawa mai zafi a cikin jam’iyyar ADC, yayin da ake sa ran zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zai gudana nan ba da jimawa ba a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen babban zaɓen 2027.