Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa yana da tabbacin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu goyon bayan ’yan Najeriya musamman daga yankin Arewa domin komawa mulki karo na biyu a zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Litinin.
Uba Sani ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarar kawo gyare-gyare a tattalin arziƙin ƙasar tun bayan hawansa mulki a 2023.
Gwamnan ya kuma soki ’yan adawa da cewa suna yawan sukar gwamnati ba tare da gabatar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin ƙasa ba.
Ya ce mutanen Arewa za su mara wa Tinubu baya saboda suna ganin kokarinsa a fannoni daban-daban.