Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da rancen Naira biliyan 3.8 domin samun guraben Hajj 3,890 ga maniyyatan jihar da za su tafi Saudiyya domin aikin Hajjin 2026.
Gwamna Dikko Radda ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin bikin bankwana da mahajjatan jihar a Katsina.
A cewar gwamnan, jihar ta fuskanci matsala wajen cike guraben Hajji da aka ware mata ta hannun hukumar NAHCON.
“An sanar da ni cewa jihar ta samu matsala wajen cike guraben Hajj da aka ware mata.”
“Saboda haka, mun amince da rancen Naira biliyan 3.8, wanda ya taimaka wajen cike guraben Hajj 3,890 na wannan shekara,” in ji shi.
Gwamna Dikko Radda ya bukaci maniyyatan su yi addu’o’i domin samun zaman lafiya, hadin kai da ingantaccen tsaro a Katsina da Najeriya yayin da suke kasa mai tsarki.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta dauki nauyin hadaya na dukkan mahajjata tare da samar musu da tallafi.
Gwamnan ya kuma bukaci mahajjata su kasance masu ladabi da mutunci yayin aikin hajji.
Ya kuma yi gargadi kan yada labaran karya yayin aikin hajji, tare da bayyana cewa an inganta gidaje da abinci ga mahajjatan jihar a Saudiyya.