Kwamitin tantance ‘yan takarar majalisar dokokin jihar Rivers na jam’iyyar APC ya hana mutane 56 shiga zaben fidda gwani da jam’iyyar ke shirin gudanarwa a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutane 98 da suka bayyana gaban kwamitin tantancewar tsakanin ranar 9 zuwa 10 ga watan Mayu, mutum 33 ne kacal aka amince da su.
Kwamitin, wanda Barista Muraine Ajibola ke jagoranta, ya bayyana cewa wadanda aka cire daga jerin ba su cika ka’idoji da sharuddan da aka gindaya domin tsayawa takara ba.
Majiyoyi sun ce mafi yawan wadanda aka hana tsayawa takarar ana alakanta su da bangaren gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, yayin da wadanda aka tantance ake ganin suna da kusanci da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Lamarin ya kara nuna yadda rikicin siyasa ke ci gaba da zurfafa tsakanin bangarorin biyu a siyasar jihar Rivers.