Hukumar Kwastam reshen jihar Kwara ta kama kilo 425.5 na tramadol da tabar wiwi, tare da shinkafar waje da sauran kayayyakin fasa kwauri da darajarsu ta haura naira miliyan 204.
An kama kayayyakin ne tsakanin watan Maris zuwa Mayun 2026, yayin da hukumar ta kuma bayyana cewa ta tara kuɗaɗen shiga na naira biliyan 3.89 a watanni ukun farkon shekarar 2026.
Hakan na zuwa duk da ci gaba da rufe iyakar ƙasa tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin.
Mukaddashin shugaban kwastam na yankin, Mataimakin Kwanturola Najeem Ogundeyi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai karo na uku da hukumar ta gudanar a Ilorin.
Ogundeyi ya ce sun mayar da hankali ne kan wuraren da aka fi yin fasa kwauri kamar Bukuro, Gurumi, Sikira, Okuta, Boriya, Tewu, Bero, Sango, Okeoyi, Alapa, Malete, Bani, Offa, Idofian, Eiyenkorin da titin Lagos zuwa Ilorin.
A cewarsa, ana sanya ido sosai a waɗannan wurare saboda yadda masu fasa kwauri ke ci gaba da ƙoƙarin shigar da haramtattun kayayyaki cikin ƙasa da fitar da su.
Ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama kilo 49.5 na tabar wiwi da kilo 376 na tramadol a ayyuka daban-daban da suka gudanar.
Sauran kayayyakin da aka kama sun haɗa da:
buhunan shinkafar waje 155 da darajarsu ta kai naira miliyan 52.4,
fakiti 3,697 na macaroni da darajarsu ta kai naira miliyan 110.9,
galan 418 na man girki da darajarsu ta kai naira miliyan 27.1.
Hukumar ta kuma ƙwace:
galan 237 na fetur ɗauke da lita 5,925,
tayoyi 70 da aka yi amfani da su,
ƙulle 18 na tsofaffin kaya,
da galan 19 na wasu sinadarai masu haɗari.
“A taƙaice, daga watan Maris zuwa yanzu, jami’an hukumar sun samu nasarar kama kayayyaki daban-daban guda tara da jimillar darajarsu ta kai naira 204,763,439,” in ji Ogundeyi.
Ya ce nasarorin sun nuna jajircewar hukumar wajen dakile haramtattun kasuwanci da kare kuɗaɗen shiga na ƙasa.
Mukaddashin shugaban ya kuma ce hukumar ta tara kuɗaɗen shiga naira biliyan 3.89 a watanni ukun farko na shekarar 2026, inda ya danganta hakan da ƙarfafa ayyukan sa ido da karɓar haraji.
Ya yi kira ga mazauna yankunan kan iyaka da su ci gaba da bai wa hukumar sahihan bayanai domin taimaka wa yaƙi da fasa kwauri.
Haka kuma ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da bin diddigin masu hannu cikin haramtattun kasuwanci tare da kare tattalin arzikin ƙasa.