Jam’iyyar ADC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daina tsoma baki cikin harkokin shari’a, tare da dakatar da duk wani yunƙuri na katsalandan a shari’ar da ke gudana tsakanin shugabancin jam’iyyar da Nafiu Bala Gombe.
Jam’iyyar, ta bakin sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ta ce ta gano wani “makirci mai tayar da hankali” daga wasu masu neman anfani da iko domin kawo cikas ga shari’ar ta hanyar matsa wa Mai Shari’a Justice Nwite ya janye daga karar.
ADC ta ce manufar hakan ita ce a mayar da shari’ar zuwa hannun wasu alkalai da ake ganin za su iya bin tasirin siyasa.
Jam’iyyar ta bayyana cewa idan aka bari hakan ta faru, zai zama babbar barazana ga mutuncin bangaren shari’a da kuma amfani da hukumomin gwamnati wajen murƙushe ‘yan adawa.
A cewar ADC:
“Bayanan da tawagar lauyoyinmu ke da su sun nuna cewa duk da cewa har yanzu ba a fitar da kwafin hukuncin Kotun Koli ba, abin mamaki an sanya ranar 8 ga Mayu, 2026 domin sauraron shari’ar a gaban Mai Shari’a Nwite.”
Jam’iyyar ta ce tana da hujjojin da ke nuna cewa wannan gaggawa wani shiri ne da aka tsara domin tilasta wa alkalin janye kansa daga karar, wanda hakan zai ba babban alkalin kotun tarayya damar mayar da shari’ar zuwa hannun wasu alkalai da ake zargin suna karkata ga tasirin siyasa.
Sanarwar ta ce wannan mataki ya saɓa wa umarnin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Koli suka bayar na cewa a gaggauta sauraron shari’ar a gaban alkalin da ya fara rikonta.
Saboda haka, ADC ta ce duk wani yunƙuri na cire shari’ar daga hannun Justice Nwite — ta hanyar matsin lamba, tsoratarwa, bata suna ko wata dabara — katsalandan ne kai tsaye cikin aikin shari’a.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga NJC, Babban Alkalin Najeriya da sauran masu kishin gaskiya a bangaren shari’a da su gaggauta shiga tsakani domin dakatar da abin da ta kira barazana ga ‘yancin bangaren shari’a.