Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi wata ganawa da takwaransa na kasar China Wang Yi a birnin Beijing.
China wadda babbar kawar Iran ce tana yin biris da takunkuman da Amurka ta kakaba, ta hanyar ci gaba da shigo da danyen mai daga Iran zuwa matatunta.
Tafiyar Mista Araghchi na zuwa ne gabanin ziyarar da shugaba Trump zai kai China a mako mai zuwa, inda zai gana da shugaba Xi Jinping.
Mista Trump ya jinkirta ziyarar tasa ne bayan da gwamnatinsa da Isra’ila suka kai wa Iran hari a karshen watan Fabrairu.