Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano za ta fara jigilar maniyyatan jihar zuwa ƙasar Saudiyya a ranar 14 ga Mayu, 2026.
Babban daraktan hukumar, Abubakar Matawalle, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin rufe taron horas da maniyyata da aka gudanar a Makarantar nazarin Larabci da ke Kano, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2026.
Ya ce:
“Bisa jadawalin da Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta fitar, Jihar Kano za ta fara jigilar rukuni na farko na maniyyata zuwa Saudiyya a ranar 14 ga Mayu, 2026, inda kamfanin jirgin sama na Max Air zai ɗauki nauyin jigilar.”
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace tun da wuri domin tabbatar da fara aikin hajjin cikin sauƙi da nasara.
A nasa jawabin, Shugaban kwamitin daraktocin hukumar, Yusuf Lawan, ya buƙaci maniyyata da su riƙa duba littattafan horaswarsu akai-akai a gida domin amfanin kansu.
Haka kuma ya shawarce su da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin da hukumomin Najeriya da na Saudiyya suka shimfiɗa a duk tsawon lokacin aikin hajjin.
Wasu hukumomin tsaro da abokan hulɗa da zasu hada hannu wajen kula da maniyatan , ciki har da Hukumar kula da shige da fice, NDLEA, Hajj tribunal, NOA, Max Air da Hisbah, na daga cikin manyan baƙin da suka gabatar da jawabai a wajen taron.