Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwankwaso ya musanta shirin barin ADC zuwa NDC

Kwankwaso ya musanta shirin barin ADC zuwa NDC

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu bai yanke hukunci ba game da makomarsa a wata jam’iyya, duk da jita-jitar da ake yadawa cewa zai sauya sheka.

Ya ce rikice-rikicen da ke cikin ADC, musamman batutuwan shari’a, sun jefa jam’iyyar cikin matsala.

Kwankwaso ya ce Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da shugabancin David Mark amma ta mayar da shari’ar zuwa kotun ƙasa, yayin da wata kotu ta soke wani taron jam’iyyar.

Haka kuma, ya ce Ministan Shari’a na Tarayya na ƙoƙarin soke rajistar jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa sun fara tattaunawa da wasu jam’iyyu kamar NDC da PRP domin duba mafita mafi kyau.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce duk wata shawara da za su yanke za su sanar da ita a hukumance nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments