Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Najeriya ta gayyaci Babban Jami’in Diflomasiyyar Afirka ta Kudu kan zargin...

Gwamnatin Najeriya ta gayyaci Babban Jami’in Diflomasiyyar Afirka ta Kudu kan zargin muzgunawa ƴan ƙasarta

Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Babban Jami’in Diflomasiyyar ƙasar Afirka ta Kudu da ke Nigeria kan hare-haren da ake kai wa ‘yan ƙasashen waje.

Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Babban Jami’in Diflomasiyyar ƙasar Afirka ta Kudu da ke Nigeria kan hare-haren da ake kai wa ‘yan ƙasashen waje.

‘Yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu na daga cikin waɗanda abin ya shafa a hare-haren da ke faruwa.

A wata sanarwa, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya ce an gayyaci mukaddashin Babban Jami’in Diflomasiyyar zuwa Abuja domin tattauna batun.

Ya bayyana cewa manufar ganawar ita ce isar da damuwar gwamnatin Najeriya kan abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan, waɗanda ka iya shafar kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.

Sanarwar ta ce:
“Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta gayyaci mukaddashin Babban Jami’in Diflomasiyyar Afirka ta Kudu domin ganawa da za a yi ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2026, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.”

Ta ƙara da cewa:
“Manufar wannan ganawa ita ce bayyana matuƙar damuwar gwamnatin Najeriya kan abubuwan da ke faruwa waɗanda za su iya shafar kyakkyawar alaƙar ƙasashen biyu.”

“Za a fi mayar da hankali wajen tattauna zanga-zangar da ƙungiyoyi daban-daban ke yi a Afirka ta Kudu da kuma rahotannin cin zarafin ‘yan Najeriya da kai hare-hare kan kasuwancinsu.”

Ma’aikatar ta ce tana sane da ƙara nuna damuwa da ‘yan Najeriya ke yi kan yadda ake mu’amala da su a Afirka ta Kudu, amma ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da jaddada cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙarin kare haƙƙoƙi da jin daɗin ‘yan Najeriya da ke zaune a can.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments