Majalisar Ɗinkin Duniya a taronta na 1993 ta ayyana kowace ranar 3 ga Mayu a matsayin ranar Ƴancin ƴan Jarida ta Duniya domin jinjina wa masu aikin jarida da da sabunta alƙawarin kare ‘yancinsu.
Taken bana shi ne, “Gina Makoma ta Zaman Lafiya”, wanda ake gani a matsayin kalubale mai nauyi kuma gargadi ga halin da ake ciki a yanzu .
Taken na tunatar da duniya cewa aikin jarida, ‘yancin faɗar albarkacin baki ne, da samun bayanai ba kayan ado na dimokuraɗiyya ba ne, illa manyan ginshiƙai ne na zaman lafiya, tsaro da ci gaba.
A wannan rana, ana sake jaddada cewa dimokuraɗiyya ba za ta rayu ba tare da ‘yancin jarida ba.
Ƙasa ba za ta zauna kalau ba tare da ‘yancin jarida ba.
Ƙungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana cewa kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu ba alatu ba ne—su ne ginshiƙin dimokuraɗiyya.
Sai dai a duniya baki ɗaya, ‘yan jarida na fuskantar zalunci da muzguna wa.
A yankin Zirin Gaza, sama da ‘yan jarida 100 sun mutu tun bayan rikicin da ya ƙaru—wanda ya sa wurin ya zama mafi haɗari ga ‘yan jarida a tarihi.
A yaƙin Ukraine ma, sama da ‘yan jarida 15 sun rasa rayukansu.
Bayan yaƙe-yaƙe ma, akwai wasu barazana kamar cin zarafi, gudun hijira da barazanar yanar gizo.
Sama da ‘yan jarida 300 a kowace shekara suna fuskantar tsoratarwa.
UNESCO ta yi gargadi cewa hare-hare kan ‘yan jarida na ƙaruwa, musamman mata, waɗanda ke fuskantar cin zarafi na musamman da kuma hari ta yanar gizo.
A Nigeria, labarin ba sabon abu ba ne.
Ana tunawa da lamarin Agba Jalingo, wanda aka kama aka tsare na tsawon watanni saboda rahotonsa kan zargin cin hanci. Wannan ya nuna yadda tambayar gaskiya ke da tsada.
Shugaban NUJ, Alhassan Yahaya Abdullahi, ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ba za ta ƙarfafa ba sai ‘yan jarida sun yi aiki ba tare da tsoro ba.
Ya kuma nuna matsalar rashin kulawa da ‘yan jarida ke fuskanta– albashi mara tsoka, rashin inshora da walwala.
Akwai kuma sabon haɗari—shari’o’i da ake amfani da su don tsoratar da ‘yan jarida, da kuma yaɗa ƙarya da fargaganda da ke lalata amincewa da sahihancin labarai.