Tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, ya sayi fom ɗin tsayawa takara domin neman kujerar Sanata ta Kano ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Wannan bayani ya fito ne a ranar Laraba ta hannun mai taimaka masa, Mansoor Man’ash, ta shafin sada zumunta, inda ya sanar da shigowar Gwarzo cikin takarar.
Sanarwar ta ce ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gwarzo da Kabo, Hon. Abdullahi Mu’azu Baban Gandu, tare da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, Hon. Hassan Garban Kauye Farawa, suna rike da fom ɗin a madadinsa.
Kujerar Sanatan Kano ta Arewa a halin yanzu na hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, wanda hakan ke nuna cewa wannan takara na iya zama daya daga cikin fafatawar siyasa mafi zafi a jihar gabanin 2027.
Gwarzo, wanda gogaggen ɗan siyasa ne kuma tsohon mataimakin gwamna, ana sa ran zai yi amfani da kwarewarsa da kuma goyon bayan jama’a a matakin ƙasa wajen fafata wannan takara, wacce masu nazari ke hasashen za ta kasance mai matuƙar zafi a cikin jam’iyyar APC.
Rahotanni sun nuna cewa wannan sanarwa ta fara jawo muhawara a tsakanin ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki, yayin da ake nazarin tasirin wannan mataki na Gwarzo ga tsarin siyasar Kano ta Arewa.
Ko da yake zaɓen 2027 bai kusa ba sosai, ana fara ganin alamun motsin siyasa tun daga yanzu, inda fitowar ‘yan takara da shirin haɗaka ke nuna cewa za a fuskanci gasa ta siyasa mai zafi a Jihar Kano.