Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Delta ta kama wani jami’i, ASP Nuhu Usman, wanda ake zargi da harbe wani mutum har lahira mai suna Mene Ogidi mai shekaru 28, a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta a yankin Effurun, ƙaramar hukumar Uvwie.
Lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Afrilu, 2026, inda bidiyon ya nuna jami’in yana yi wa wanda ake zargin tambayoyi kafin daga bisani ya bude masa wuta, inda ya mutu nan take.
Bidiyon ya kuma nuna wasu jami’an ‘yan sanda suna ɗaukar gawar tare da saka ta cikin motar ‘yan sanda kirar Hilux kafin su bar wurin.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a jihar, Bright Edafe, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa kwamishinan ‘yan sanda, Yemi Oyeniyi, ya yi Allah-wadai da wannan lamari, yana mai bayyana shi a matsayin kisan kai ba tare da bin doka ba.
Ya ce jami’an sun kama mutumin ne bisa wani rahoton sirri, inda ake zargin an kama shi yana kokarin safarar wani kunshi da ke dauke da bindiga kirar Beretta tare da harsasai guda hudu.
Sai dai ya bayyana cewa ASP Usman ya karya dokar aiki ta ‘yan sanda da kuma ka’idojin aiki na yau da kullum, ta hanyar harbe mutumin, wanda hakan ya jawo mutuwarsa.
Ya kara da cewa an kama jami’in, an yi masa tambayoyi, sannan an tura shi zuwa hedikwatar ‘yan sanda a Abuja domin gurfana gaban kwamitin ladabtarwa na rundunar, inda za a dauki matakin hukunci cikin gaggawa, ciki har da yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani aiki na rashin bin doka, sakaci ko kisan kai ba tare da bin ka’ida ba daga jami’anta, tare da tabbatar da cewa za a yi adalci.
Haka kuma ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, yana mai cewa ana daukar karin matakai domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a lamarin.