Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi bayan wani rikici mai muni da ya faru a yankin Gyadi-Gyadi tsakanin ƙungiyoyin ‘yan daba masu gaba da juna.
A cewar ‘yan sandan, jami’ansu sun yi gaggawar kai dauki bayan samun kiran gaggawa cewa wasu ‘yan daba sun taru domin fafatawa a yankin.
Da isar su wurin, jami’an sun tarar da masu rikicin suna arangama da juna, inda aka lalata motar daukar marasa lafiya, kuma aka yi yunkurin kai hari wasu wurare.
Rahoton ya ce ‘yan sandan sun yi nasarar dakile rikicin tare da maido da zaman lafiya a yankin, kodayake ‘yan daban sun sake taruwa suna kai hari ga jami’an tsaro da makamai masu hadari da duwatsu.
Rundunar ta tabbatar da cewa an kama mutum shida daga cikin wadanda ake zargi, yayin da ake ci gaba da bincike domin kamo sauran da suka tsere da kuma tabbatar da wadanda ke da hannu a rikicin.