Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMutum 2 zuwa 3 na mutuwa a kullum saboda sanƙarau a kauyen...

Mutum 2 zuwa 3 na mutuwa a kullum saboda sanƙarau a kauyen Sokoto

Mazauna wani gari sun nuna damuwa kan zargin barkewar cutar sanƙarau wadda ke kashe mutane, a ƙauyen Kurawa, ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. Yara da matasa ne suka fi kamuwa da cutar.

Mazauna wani gari sun nuna damuwa kan zargin barkewar cutar sanƙarau wadda ke kashe mutane, a ƙauyen Kurawa, ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.
Yara da matasa ne suka fi kamuwa da cutar.

Majiyoyi daga cibiyar lafiya ta ƙauyen sun ce lamarin ya ƙara tsananta a kwanakin baya, inda ake samun mace-mace kusan biyu zuwa uku a kullum, galibi tsakanin masu shekaru 2 zuwa 20.
Sun ƙara da cewa ana samun yawaitar marasa lafiya da ke zuwa asibiti domin neman magani, yayin da tsoro ya mamaye al’umma saboda wata “cuta da ba a san asalinta ba.”

“Mutane suna tururuwa zuwa asibiti kullum domin neman magani. Mun cika sosai kuma ba mu san abin da ke kashe mutane kusan kowace rana ba,” in ji ɗaya daga cikin majiyoyin.

Sun ce da yawa daga cikin waɗanda suka kamu suna mutuwa kafin a tantance cutar yadda ya kamata, sannan an ba jama’a shawarar su guji kwanciya a ɗakuna masu zafi da kulle tagogi saboda yanayin zafi da ake ciki.

Mazaunan sun bayyana alamomin cutar da suka haɗa da suma, matsanancin ciwon wuya, amai, gudawa, zazzabi mai zafi, da kuma fitar kumfa daga baki a wasu lokuta–duk waɗannan na cikin alamomin sankarau.

“A lokuta, yaro zai fara da kuka da ciwon wuya kafin ya suma,” in ji wani daga cikin majiyoyin.

Duk da matakan da aka ɗauka, mazaunan sun nuna damuwa cewa cutar ba ta ragu ba, lamarin da ya sa wasu ke zargin wata cuta dabam ce.

“An gaya mana sankarau ne, amma cutar ba ta tsaya ba. Wannan ne ya sa mutane ke tunanin wata cuta dabam ce,” in ji wani mazaunin garin.

Sai dai wata majiya daga asibiti ta ce mutuwar mutum uku kacal aka tabbatar a asibitin, tana mai cewa yawancin mutanen sun mutu ne a gidajensu. Ta kuma ƙara da cewa da yawa suna mutuwa cikin awanni 24 bayan fara alamomin cutar.

Sarkin ƙauyen, Mudassir Abdullahi Kurawa (Wakilin Malumfashin Kurawa), ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ana zargin sankarau ne.

“A cikin garinmu kaɗai, kusan mutane 10 zuwa 15 sun mutu, ba tare da lissafa waɗanda ke ƙauyukan da ke kewaye ba. Yawancinsu yara ne masu shekaru tsakanin 2 zuwa 10,” in ji shi. Ya ƙara da cewa barkewar cutar ta fara kusan makonni uku da suka gabata.

Ya kuma ce a ranar Asabar kaɗai, an kwantar da marasa lafiya 15 a asibiti, kuma uku daga cikinsu sun mutu nan take.

A halin yanzu, Kwamishinan Lafiya na Jihar Sokoto, Faruk Abubakar Wurno, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ya samu rahoton ne a ranar Lahadi.

“Na samu rahoton a ranar Lahadi, nan take na tura ma’aikatan lafiya domin bincike da kuma bayar da magunguna kyauta,” in ji shi.
Sai dai ya ce har yanzu ba a tantance ainihin yawan mutanen da suka mutu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments