Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeƳan Najeriya na fuskantar barazana a Afirka ta Kudu, suna roƙon gwamnati...

Ƴan Najeriya na fuskantar barazana a Afirka ta Kudu, suna roƙon gwamnati ta dauki mataki

‘Yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu sun bayyana cewa suna fuskantar ƙarin barazana sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi, inda suka nemi gwamnatin tarayyar Najeriya ta gaggauta daukar matakan kare su.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan Najeriya na rayuwa cikin tsoro sakamakon hare-hare da barazanar da ake yi musu, ciki har da lalata kadarorinsu da kuma kai musu hari a wuraren zama da kasuwanci.

Wasu daga cikin su sun ce suna karɓar sakonnin barazana, yayin da wasu ma suka fara tunanin barin ƙasar domin tsira da rayukansu.

Kungiyoyin ‘yan Najeriya a can sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta shiga tsakani ta hanyar tattaunawa da gwamnatin Afirka ta Kudu domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasar.

Haka kuma sun bukaci hukumomin Afirka ta Kudu su dauki tsauraran matakai kan masu aikata irin wadannan hare-hare domin dakile yaduwar lamarin.

Wannan matsala ta kin jinin baki ba sabuwa ba ce, domin a baya ma an samu hare-hare da suka haddasa asarar rayuka da dukiyoyi na ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashen Afrika a Afirka ta Kudu.

A halin yanzu, ana ci gaba da nuna damuwa cewa idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, lamarin na iya kara muni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments