Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƳan bindiga sun hallaka Ministan tsaron Mali, Sadio Camara

Ƴan bindiga sun hallaka Ministan tsaron Mali, Sadio Camara

An tabbatar da mutuwar Sadio Camara sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai.

Ministan tsaron Mali, Sadio Camara, ya rasu sakamakon wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai gidansa da ke kusa da babban birnin ƙasar, Bamako, a ranar Asabar.

Harin na ɗaya daga cikin jerin hare-hare da masu ɗauke da makamai da kuma ‘yan awaren Tuareg suka kai a wasu birane daban-daban a lokaci guda.

Rahotanni sun bayyana cewa tsawon shekaru kenan ƴan awaren na Tuareg da a aka fi sani da FLA ke ta ƙokarin ɓallewa don kafa na su shugabancin, a wannan yanki, lamarin da ya sa suka haɗa kai da ƙungiyar JNIM mai akala da Alqa’eda wadda ita kuma manufarta ita ce yana manufarta a yankin wajen kai waɗannan hare hare.

A yanzu dai ƴan tawayen na Tuareg sun ce suna riƙe da garin Kidan, mai muhimmanci na yankin hamada, inda wata rundunar tsaron Rasha ke da sansani.

Haka kuma an kai hari gidan shugaban mulkin sojin kasar Assimi Goïta, amma bai samu wani rauni ba.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments