Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiRikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutane sama da 40 a gabashin Chadi

Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutane sama da 40 a gabashin Chadi

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da 40 a rikicin ƙabilanci da ya auku a gabashin Chadi.

Jami’an gwamnati a ƙasar Chadi, sun ce aƙalla mutane arba’in da biyu ne suka mutu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙabilu a gabashin ƙasar.

An yi imanin cewa tashin hankalin da ya faru a lardin Wadi Fira, ya samo asali ne daga taƙaddama kan wata rijiyar ruwa, lamarin da daga bisani ya haifar da jerin hare haren ramuwar gayya a faɗin yankin.

Mataimakin firaministan ƙasar, Limane Mahamat, ya shaida wa gidan talabijin ɗin ƙasar cewa yanzu an shawo kan lamarin.

Gabashin Chadi dai ya daɗe yana fama da rikice-rikicen kabilanci tsakanin manoma da larabawa makiyaya tsawon shekaru.

Sai dai kuma rikicin ya ƙara tsananta sakamakon ƙarancin albarkatu da matsalolin tsaro, musamman bayan kwararar ‘yan gudun hijira sakamaon yaƙin basasar Sudan.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments