Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugaba Trump ya tsallake rijiya da baya daga harin bindiga a fadar...

Shugaba Trump ya tsallake rijiya da baya daga harin bindiga a fadar White House

Fadar White House ta Amurka ta tabbatar da cewa shugaban ƙasar Donald Trump na cikin ƙoshin lafiya, bayan da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta a cikin fadar dai-dai lokacin da shugaban ke gudanar da liyafar cin abincin dare tare da ƴan jaridar fadar shugaban ƙasar.

Wani jami’in hukumar FBI ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa maharin ya buɗewa jami’in rundunar tsaron cikin gidan wuta, kafin daga bisani ya fara harbin kan mai uwa da wabi.

Sai dai kuma bayan sa’oi biyu da harin shugaba Trump ya ce jami’in cikin gidan da aka harba ya tsira, kasancewar yana sanye da rigar kariya ga harsashi.

Tuni dai jami’an tsaro suka kama maharin da shugaba Trump ya kwatanta da mara hankali.

Bayanai sun ce ba’a yi asarar rai a yayin wannan hari mai cike da ban mamaki ba.

Bayan chaje maharin an same shi da ƙananan bindigu cike da harsasai a ƙugunsa, kuma tuni jami’an tsaron sirri suka tafi da shi ofishinsu don faɗaɗa bincike.

Jami’an tsaro sun ce binciken su na farko ya gano cewa maharin ya aikata laifin ne bisa raɗin kansa ba tare da haɗa kai ko shirya shi da wani ba.

Tuni jami’an tsaro su ka fara bincike a birnin California, asalin garin ɗan bindigar, kamar yadda Anthony Guglielmi, mai magana da yawun rundunar tsaron sirri na ƙasar ya shaida.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments