Wani labari da ya yadu a kafafen sada zumunta ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano ta raba dan-kamfai ga mata a matsayin tallafi ko kuma kyautar siyasa.
An yaɗa wannan zargi ne tare da hotunan wasu mata da ke riƙe da jajayen ɗan-kamfai, tare da rubuce-rubuce da ke nuna cewa gwamnati ce ta ba su.
A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa
ya nuna binciken da aka gudanar ya nuna cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne.
An yi amfani da wata hanya ta fasaha da ake kira Error Level Analysis ELA domin binciken hotunan, kuma sakamakon ya nuna cewa an gyara hotunan ne ta hanyar haɗa wasu abubuwa daban-daban a ciki.
Binciken ya gano cewa hotunan sun samu sauyi, inda aka saka hoton gwamna a kan ɗan-kamfai domin a nuna kamar shi ne ya raba su.
Haka kuma, an gano cewa asalin hotunan sun fito ne daga wani bidiyo na wasu magoya bayan siyasa da suka nuna ɗan-kamfai a matsayin wani salo na nuna goyon baya ko sukar abokan hamayya, ba wai wani shirin gwamnati ba.
An kuma lura cewa labarin “raba ɗan-kamfai a matsayin empowerment” ya fara yaduwa ne bayan wannan bidiyo, wanda ke nuna cewa an karkatar da gaskiya ne daga abin da ya faru a zahiri.
Zargin cewa gwamnatin Kano ta raba kayan ciki ga mata a matsayin tallafi ko kyautar siyasa ba gaskiya bane. Hotunan da aka yada an gyara su ne domin yaɗa bayanan da ba su da gaskiya.