Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKowane ɗan Najeriya ana binshi bashin Naira dubu 724

Kowane ɗan Najeriya ana binshi bashin Naira dubu 724

Jimillar bashin da ofishin kula da basussuka na ƙasa ya bayyana ya nuna cewa bashin gwamnatin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025. Wannan yana nufin cewa idan aka raba bashin, kowane ɗan ƙasa yana da nauyin kusan Naira 724,000.

Jimillar bashin da ofishin kula da basussuka na ƙasa ya bayyana ya nuna cewa bashin gwamnatin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025. Wannan yana nufin cewa idan aka raba bashin, kowane ɗan ƙasa yana da nauyin kusan Naira 724,000.

Sabbin bayanan sun nuna cewa bashin ƙasar na ƙaruwa a hankali, musamman saboda ƙarin aro na cikin gida. Haka kuma, wannan adadi bai haɗa da sabon bashin Naira tiriliyan 8.3 da aka amince da shi daga ƙasashen waje ba, wanda ke nuna cewa bashin zai iya ƙaruwa a nan gaba.

Da yake yawan jama’ar Najeriya ya kai kusan miliyan 220, hakan na nufin kowane ɗan ƙasa yana ɗauke da wani ɓangare na wannan bashin a kansa.

Bincike ya kuma nuna cewa bashin cikin gida shi ne mafi yawa, yana da kaso 53.27, wanda ya kai Naira tiriliyan 84.85. Gwamnatin tarayya ce ke da mafi yawan wannan bashin, yayin da jihohi da babban birnin tarayya suka ɗauki wani ɓangare kaɗan.

Bashin waje kuwa ya kai Naira tiriliyan 74.43 wato kaso 46.73, wanda shi ma ya ƙaru idan aka kwatanta da watannin baya.

Wannan ci gaba na karuwar bashi ya jawo damuwa kan yadda ƙasar za ta iya ci gaba da biyan bashin, musamman ganin yadda kuɗin shiga na gwamnati ke fuskantar matsin lamba.

Masani a fannin kuɗi, Paul Alaje, ya bayyana cewa wannan bashin duk ’yan Najeriya ne za su biya shi, har ma da waɗanda ba a haife su ba yanzu.
Ya kara da cewa, yayin da bashin ke ƙaruwa, haka ma kuɗin biyan bashin ke ƙaruwa, ana kuma biyan bashin ne ta hanyar haraji da sauran kudaden shiga na gwamnati.
Idan bashin ya ɗauki lokaci mai tsawo, har ’yan baya za su biya.

Ya kuma nuna cewa hauhawar farashi wanda ya ƙaru zuwa kashi 15.38 yana ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga ’yan ƙasa.

A cewar sa, gwamnati na ci gaba da aro ne saboda buƙatun ƙasa sun fi kuɗin shiga yawa. Duk da cewa ana samun kuɗi, amma ba ya wadatar da buƙatun gaggawa kamar biyan albashi, gina hanyoyi, da kuma samar da wutar lantarki.
Saboda haka, dole ne gwamnati ta ci gaba da aro domin cike gibin da ke akwai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments