Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeMutane 9 sun mutu a harin makaranta na biyu cikin kwanaki 2...

Mutane 9 sun mutu a harin makaranta na biyu cikin kwanaki 2 ƙasar Turkiyya

Akalla mutane tara ne suka mutu, yayin da wasu 13 suka jikkata a wani harin bindiga da aka kai a makarantar Ayser Çalık Middle School da ke Kahramanmaraş a tsakiyar kasar Turkiyya a ranar Laraba, bayan wani ɗalibi ya bude wuta.

Akalla mutane tara ne suka mutu, yayin da wasu 13 suka jikkata a wani harin bindiga da aka kai a makarantar Ayser Çalık Middle School da ke Kahramanmaraş a tsakiyar kasar Turkiyya a ranar Laraba, bayan wani ɗalibi ya bude wuta.

Hakan ya sa wannan ya zama hari na biyu a makarantu cikin kwanaki biyu a ƙasar.

Gwamnan Kahramanmaraş, Mukerrem Unluer, ya ce mutum huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata na cikin tiyata.
Ya kuma bayyana cewa wani malami na daga cikin waɗanda suka mutu a harin.

Bayan harin, wanda ya kai harin ya kashe kansa, kamar yadda gwamnan ya shaida wa manema labarai a wurin da lamarin ya faru.

Ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta Turkey ta hana yada labarai game da harin domin kare binciken da ake yi.

Ministan shari’a, Akin Gurlek, ya ce an tura masu gabatar da ƙara guda bakwai domin gudanar da bincike kan lamarin.

A baya, an ruwaito cewa a ranar Talata, akalla mutane bakwai ciki har da ɗalibai sun jikkata a wani harin bindiga a wata makarantar sakandare a yankin Siverek da ke lardin Sanlıurfa Province, inda wani mutum ya shiga makarantar dauke da bindiga ya fara harbi ba kakkautawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments