Dakarun rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Wutar Daji sun samu gagarumar nasara bayan gudanar da wani samame a dajin Kumbodoro da kauyen Kumbodoro a Jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa farmaki ya jawo wa ‘yan bindigan da ke fakewa a cikin dazukan koma baya kan shirin kai hare-hare da suke yi.
Rahoton ya kuma nuna cewa dakarun sun yi nasarar wargaza maboyar ‘yan bindiga da dama, ciki har da sansanonin Azuge da suka yi kaurin suna a yankin dajin Kumbodoro.
Tare da goyon bayan rundunar sojin sama, dakarun Najeriya sun kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar tare da rusa muhimman cibiyoyin ayyukansu, lamarin da ya rage karfinsu na barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Haka kuma, dakarun Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane takwas da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su suna neman kudin fansa.