Mataimamin shugaban Amurka JD Vance ya zargi gwamnatin Iran da abin da ya kira ta’addanci na tattalin arziki saboda rufe mashigar Hormuz ta hana jiragen ruwa bi.
Ya ce Shugaba Trump ya nuna – kamar yadda ya ce – shi ma kwallo ne – a kan wannan harka.
A jiya Litinin ne dai Amurka ta fara aiwatar da abin da ta kira – datse jiragen ruwa ta hana su amfani da tasoshin ruwa na Iran.
Ya zargi Iran da tsilla-tsilla a lokacin tattaunawar ta karshen mako , inda ya ce yana sa ran Iran ta bude mashigar gaba daya, ita kuma a saka mata da dakatar da bude wuta.
Hakan dai ya biyo bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar zaman lafiya ta Iran da Amurka a Pakistan.
Amma kuma duk da haka mataimakin shugaban na Amurka ya sheda wa kafar yada labarai ta Amurka Fox News cewa an samu cigaba sosai a tattaunawar.