Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSERAP ta yi kira ga Majalisa da ta binciki zargin alakar shugaban...

SERAP ta yi kira ga Majalisa da ta binciki zargin alakar shugaban INEC da APC

Kungiyar SERAP ta nemi Majalisar Tarayya da ta binciki ko akwai wata alaƙa tsakanin shugaban INEC da jam’iyyar APC.

Kungiyar kare hakkin jama’a da yaki da rashawa ta SERAP ta bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta fara cikakken bincike kan zarge-zargen da suka shafi shugaban INEC.

A ƴan kwanakin nan ne aka gano wasu sakonnin goyon bayan APC a kafafen sada zumunta da ake dangantawa da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu, 2026 SERAP ta roki ‘yan majalisar da su yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba su wajen gudanar da bincike.

Kungiyar ta bayyana cewa batun ba wai kawai rikici ne na kafafen sada zumunta ba, illa yana da alaka da sahihanci da kuma yadda ake kallon hukumar zabe ta INEC a idon jama’a.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments