Jam’iyyar ADC ta bukaci Farfesa Joash Amupitan ya sauka daga mukaminsa na shugaban INEC.
Jam’iyyar adawar ta yi wannan kira ne yayin da take martani kan sabbin zarge-zargen da ake yi masa, musamman game da tsofaffin sakonnin da aka ce ya wallafa a shafukan sada zumunta da ke nuna goyon baya ga jam’iyyar APC.
A baya, mai magana da yawun shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya gargadi jama’a kan masu ƙirƙirar asusun bogi da ke yada bayanan ƙarya, yana mai jaddada cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da zaɓe nagari.
Sai dai rikicin ya ƙara ɗaukar hankali bayan wani masani dan Najeriya da ke zaune a Amurka, Farooq Kperogi, ya wallafa wani rubutu da ke nuna wasu tsofaffin sakonni da ake zargin na Amupitan ne, waɗanda ke nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda ra’ayoyin jama’a suka rabu biyu kan sahihancin zargin da kuma tasirinsa ga amincin hukumar zaɓe.
Da yake mayar da martani, kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ba ƙaramin abin damuwa ba ne, yana mai cewa dole ne shugaban hukumar zaɓe ya kasance mai cikakken ‘yanci kuma a bayyane yake hakan ga kowa.
Ya ƙara da cewa duk wani yunƙuri na ɓoye hujjoji ko canza bayanai barazana ce ga gaskiya da dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa Amupitan bai cika ƙa’idojin da ake buƙata ba.
Saboda haka, jam’iyyar ADC ta bukaci Amupitan ya yi murabus nan take, tare da gargadin cewa za su ƙara tsaurara matakan “rashin biyayya ga gwamnati” har sai ya sauka daga mukamin nasa.