Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMusulmi sun kai wa makwabtansu kiristoci ziyarar godiya bisa ceto wani matashi...

Musulmi sun kai wa makwabtansu kiristoci ziyarar godiya bisa ceto wani matashi a Jos

A kokarin rage tashin hankali a birnin Jos, babban birnin Jihar Plateau, al’ummomin Musulmi da Kiristoci na Gangare da Shaka sun hadu domin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakaninsu.

A kokarin rage tashin hankali a birnin Jos, babban birnin Jihar Plateau, al’ummomin Musulmi da Kiristoci na Gangare da Shaka sun hadu domin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakaninsu.

Taron ya gudana ne a ranar Alhamis, inda Musulman Gangare suka kai ziyara ga al’ummar Shaka yankin da Kiristoci suka fi yawa domin gode musu bisa ceton rayuwar wani matashi Musulmi mai sana’ar kwashe shara, wanda wasu fusatattun matasa suka so kashewa a ranar Laraba.

A cewar al’ummar Musulmi, shugabanni da matasan Shaka sun taka muhimmiyar rawa wajen kare wannan matashi tare da mayar da shi lafiya ga iyalansa a Gangare.

Da yake jawabi yayin ziyarar, daya daga cikin shugabannin Musulmi, Ibrahim Kabir, ya ce manufar ziyarar ita ce nuna godiya bisa wannan kyakkyawan aiki, yana mai cewa shugabannin Shaka sun yi amfani da hikima wajen ceton rayuwar matashin.

Ya kara da cewa irin wannan hadin kai ya taba faruwa a Gangare, inda shugabanni suka dakile wasu matasa da ke kokarin kai hari kan Kiristoci, yana mai kira ga sauran al’umma da su yi koyi da hakan.

A nasa bangaren, shugaban gargajiya na Shaka, Da John Rwang Gyang, ya ce dukkan mutane daga Annabi Adam da Hauwa’u suka fito, don haka kowa daya ne, yana mai jaddada cewa babu wani addini da ke koyar da kashe wanda ba na addininka ba.

Ya ce sun yi farin ciki da ziyarar, kuma ba sa son zubar da jini a yankinsu, tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya.

Dukkan shugabannin bangarorin biyu sun yi kira ga matasa da su kasance masu bin doka da oda, tare da rungumar zaman lafiya a kowane lokaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments